Rahotanni sun bayyana cewa a watan da ya gabata ne Nneka Ede, ta sayi kungiyar kwallon kafa ta Lusitano Ginásio Clube, Futebol, SAD da ke kasar Portugal, wadda ke fafata gasar ajin lig mataki na 3 na kasar wato Campeonato de Portugal.
Rahotanni sun bayyana cewa a watan Yunin da ya gabata ne ‘yar kasuwar ‘yar asalin Najeriya ta sami kai ga mallakar kungiyar mai tarihin shekaru 108 da kafuwa.
A jawabin da ta yi bayan kammala yarjejeniyar sayen kungiyar, Nneka Ede ta bayyana matukar farin ciki akan lamarin, wanda ta ce zai kara dankon zumunci da dangantaka tsakanin kasarta Najeriya da kuma Portugal.
Haka kuma ta sha alwashin cewa wannan zai ba da gudummuwa wajen karfafawa matasan ‘yan wasan Najeriya da ke fuskantar kalubale na rashin gata domin samun fita kasashen Turai, duk kuwa da dimbin baiwa da kwarewar da su ke da ita a fagen tamaula.
A bangare daya kuma kungiyar ta fitar da sanarwa da ke tabbatar da kammala yarjejeniyar sayen kungiyar da ‘yar Najeriyar mai matukar sha’awar wasanni, wadda suka ce an dauki tsawon watanni ana yi kafin a cimma matsaya.
Ede ta kasance ‘yar Najeriya ta biyu da ta mallaki kungiyar kwallon kafa a Turai, bayan da wani dan kasuwa Kunle Soname ya sayi kungiyar Deportivo can baya a shekara ta 2015.
Facebook Forum