‘Yan sandan kwantar da tarzoma sun harba bokonon tsohhuwa akan magoya bayan ‘yan adawa a rumfunan zaben shugaban kasar da aka yi jiya Lahadi. Dimbin ‘yan sandan da aka jibge a Brazzaville babban birnin ne suka tarwatsa jama’a.
An dai fara kidayar kuri’un da aka kada a zaben da ake tsammanin tazarcen dadadden shugaban kasar Denis Sassou Nguesso da ke neman shekaru 30 yana mulkin kasar. A shekaran jiya ne dai aka bada umarnin katse layukan wayar kasar har a gama zaben.
Ministan cikin gidan kasar Raymond Zhephirin Mbolou ne ya sanar da manyan kamfaninin wayar sadarwar kasar game da cewa, baya ga yin waya har sakon kar ta kwana na text ba a yarda a yi ba saboda dalilan tsaro.
An sami kwafin takardar umarnin wannan doka a shafin sadarwar internet, sai dai an rubuta wasu lambobin da su kadai ne zasu iya karbar waya ko sakonni a lokacin zaben na jiya. Janar Jean Marie mai ritaya ne babban dan hamayyar neman shugabancin kasar.