Da shigan 'yanbindigan garin suka dinga bankawa gidaje wuta tare da harbin kan mai uwa da wabi.
Yanayin ya sa mazauna garin sun fice zuwa wasu wurare daban domin tsira da rayukansu. Idan ba'a manta ba ranar 30 ga watan Mayu wasu 'yanbindiga suka kashe sarkin garin na Gwoza.
Wata guda ke nan da 'yanbindiga suka cafke garin Damboya lamarin da ya sa babu wanda zai iya bin hanyar Maiduguri zuwa garin ko zuwa Biu. Yanzu da suka kama Gwoza sun rufe yankin ke nan.
Wani da ya samu ya arce daga garin da yanzu yana kan dutse ya zanta da wakilin Muryar Amurka amma bai yadda a ambaci sunansa ba. Yace tun jiya wajen karfe biyar suka farma garin inda suka fafata da sojoji kafin su fatattakesu su kwace garin. 'Yanbindigan sun mamaye garin kamar yadda suka yiwa Damboa.
Akwai rahoton cewa an kashe mutane da dama. Duk da wai an ce an tura sojoji zuwa garin amma wanda ya zanta da wakilin Muryar Amurka yace basu ga wani soja ba.
Harin shi ne mafi muni duk da ikirarin da jami'an tsaro keyi.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.