An fara gasar cin kofin Nahiyar kasashen Afrika na 'yan kasa da shekaru sha bakwai (Under 17) wanda ya ke gudana a kasar Tanzaniya na shekarar 2019.
Mai masaukin baki ce Tanzaniya ta bude gasar tsakanita da tawagawar Golden Eaglet na Najeriya, inda Najeriya ta samu nasar da kwallaye 5 da 4 a wasan da akayi ranar Lahadi 14 ga watan Afirilu bana a filin wasa na Dar es
Salaam.
Kana shine wasa na farko da akafi zura kwallaye masu yawa a tarihin gasar, inda jimillar kwallayen da kasashen biyu suka zurara suka kai tara.
Da yake jawabi wa manema labarai bayan tashi a wasan, kocin kasar Tanzaniya Oscar Milambo ya zargi 'yan wasansa kan rashin dai-daituwa a yayinda suke wasan na daya daga cikin abunda ya basu matsala har aka doke su.
Dan wasan Najeriya mai suna Akinkunmi Amoo, wanda ake masa lakani da Messi mai sanye da riga lamba 13, shi ne ya samu lambar yabo na gwarzon dan wasan da yafi kokari a wasan da aka buga wato Best Player of the Match, inda kamfanin da ya dauki nauyin gasar wato Total, ya bashi lambar yabo bayan an tashi a wasan.
Tawagar Golden Eaglet zata buga wasanta na gaba amatakin rukuni ranar Laraba tsakanita da kasar Angola.
Facebook Forum