An sanya sunayen ‘yan wasan kwallo biyu kuma ‘yan asalin Najeriya, Tosin Adarabioyo da Eberechi Eze cikin sabon rukunin Gwarazan Kwallo na EFL na mako, wanda wani shafin yanar gizo mai girmama ‘yan kwallo ya bayyana, bayan da aka kammala wasanni a ranar Lahadi 8 ga Disamba.
Ba abin mamaki ba ne cewa Eze ya na cikin kwararrun 'yan wasa goma sha daya a gasar, bayan da suka ci Preston North End 2-0.
Dan wasan tsakiya na Manchester City Adarabioyo, ya nuna kwazonsa yayin da Blackburn Rovers ta ci wasa na hudu a jere, in da ta doke Derby County 1-0.
Yayin da Adarabioyo ya kasance daya daga cikin masu tsaron baya a tsakiya da ci 4-4-2, Eze ya dauki matsayi a cikin matsakaicin dan wasan gaba na zahiri.
Adarabioyo ya fara wasa a karo na 11 a farkon kakar, ya yi nasarar lashe wasanni guda biyar.
Eze yana da darajar 8.7 daga cikin goma kuma Adarabioyo ya sami 7.8 saboda kokarinsa.
Facebook Forum