Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Tawayen Kungiyar MJRN Sun Mika Wuya Ga Gwamnatin Sojin Nijar


Gwamnan jihar Agadas Birgediya Janar Ibrah Issa Bulama lokacin mika makamai da wuya na wasu ‘yan tawayen kungiyar MJRN
Gwamnan jihar Agadas Birgediya Janar Ibrah Issa Bulama lokacin mika makamai da wuya na wasu ‘yan tawayen kungiyar MJRN

Daruruwan ‘yan tawaye na kungiyar MJRN dake fafutukar ganin an dawo da tsohon shugaba Mohamed Bazoum da sojoji suka kifar a shekarar 2023 da suka fito daga kasar Libiya sun ajiye makamai tare da mika wuya ga mahukuntan kasar Nijar

Makaman da ‘yan tawayen suka mikawa hukumomi sun hada da manya da kananan makamai da kuma alburusai

Lokacin da wasu ‘yan tawaye suka mika makamai da wuya a Nijar
Lokacin da wasu ‘yan tawaye suka mika makamai da wuya a Nijar

'Yan tawayen sun ajiye makamansu yayin wani biki da aka gudanar karakashin jagorancin gwamnan jihar Agadas Birgediya Janar Ibrah Issa Bulama.

Ta hanyar wani kwamiti ne dake shiga tsakani wanda gwamnatin mulkin sojojin Nijar ta kafa mai mambobi 17 da ta daurawa alhakin shawo kan ‘yan tawayen domin rungumar zaman lafiya, kwamitin ya yi nasarar wayar da kan wadannan ‘yan tawayen da suka ajiye makamansu, da kuma muhimmancin da zaman lafiya ke da shi a cikin kasa.

Wasu ‘yan tawaye da suka mika makamai da wuya a Nijar
Wasu ‘yan tawaye da suka mika makamai da wuya a Nijar
‘Yan tawaye da suka mika makamai da wuya a Nijar
‘Yan tawaye da suka mika makamai da wuya a Nijar

A kwanakin da suka gabata ne wasu manyan jiga-jigen kungiyoyin tawayen, ciki har da kakakin kungiyar tare da wasu kwamandoji uku suka bar fafutukar, tare da cewa sun yanke shawarar zaman lafiya.

To sai dai kungiyoyin fafutuka na ganin dole ne gwamnatin Nijar ta yi taka tsantsan da kuma sanya ido sosai a kan tsofaffin ‘yan tawayen domin gudun kar a koma gidan jiya inji Abdourahmane Bianou wani ‘dan fafutuka a Agadas.

Makaman wasu ‘yan tawaye da suka mika wuya a Nijar
Makaman wasu ‘yan tawaye da suka mika wuya a Nijar
Hukumomin Nijar lokacin da wasu ‘yan tawaye suka mika makamai da wuya
Hukumomin Nijar lokacin da wasu ‘yan tawaye suka mika makamai da wuya

Wannan sabon mataki na mika wuya da ‘yan tawayen ke yi da kuma rungumar zaman lafiya ya kawo sabon fata da gwamnatin Nijar ke yi na inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin kasar.

Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:

 ‘Yan Tawayen Kungiyar MJRN Dake Fafutukar Ganin An Dawo Da Mohamed Bazoum Sun Mika Wuya.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG