Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi kashedi ga 'yan ta'adda da masu tada zaune tsaye a duk fadin kasar cewa gwamnatinsa zata saka kafar wando daya da duk wanda cinikinsa shine fitina. Shugaban na Najeriya ya furta haka ne a jawabinsa na murnar cika Najriya shekaru 58 da samun 'yancin kai daga hanun turawan mulkin mallaka na Ingila.
Shugaba Buhari wanda yake yaba irin ci gaba da aka samu wajen yakin da 'yan ta'addan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya, yace bisa dukkan alamu an fara samun daidaito a yankin, kuma gwamnati ba zata gajiya ba har sai ta-ga bayan 'yan ta'adda.
Da ya juya kan mahimmancin wannan rana Shugaba Buhari yace "Yau ranar daya ga watan Oktoba, rana ce ta tunawa da samun 'yancin kai ita ce kuma jajiberen zaben kasa dake karatowa, inji shugaban Nigeria, Muhammad Buhari.
Shugaban ya ci gaba da cewa yakamata mu yi nazari akan abubuwan da suka hadamu tare da karfin da muke dashi wanda ya samo asali daga wurare daban daban da muka fito, wato mutane masu al'adu da harsuna daban daban.
A matsayina na kwamandan askarawan kasan nan maza da mata, ina ba su tabbacin cewa zan ci gaba da karfafa musu guiwa tare da basu horo, da ingantattun kayan aiki domin su sami nasara a bakin daga. Yanzu haka ina duba matsalolin da suka shafi hakkokinsu da jin dadinsu da na iyalansu,inji Shugaba Buhari.
Rikicin makiyaya da manoma da ya ki ci ya ki cincewa, wasu ne suke kokarin rarraba kawunan al'ummomin kasar su shuka kiyayya domin cimma muradun kansu, amma muna duba lamarin da zummar kawo karshensa. Saboda haka muna yabawa kungiyoyin al'umma da gwamnatocin kananan hukumomi da na jihohi da shugabannin addinai kan kokarin da suke yi na kawo karshen matsalar.
Yyinda muke tuntubar makwaftan mu da suma suke fuskantar irin wannan matsala ta makiyaya da manoma, domin mu hada karfi da karfe mu dakile matsalar. Zan yi amfani da wannan dama inja kunnuwan wadanda suke daukan makamai suna kare makiyaya ko manoma cewa su kuka da kansu domin zasu hadu da fushin hukuma. Saboda haka ina kira ga masu son zaman lafiya su yi watsi da duk wani kira ciki ko a wajen kasar su tada hankali.
Akan yaki da cin hanci da rashawa, zarmiya da wawure dukiyoyin al'umma muna kwato dukiyoyin da aka sace duk da irin turjiya da muke samu. Yadda ake wawurar biliyoyin Nairori can da, yanzu ba bu shi. Satar mai da kwangilar bogi ta mai da ake yi da yanzu babu su.
Saboda haka, kuma abu ne da ake gani karara, gine ginen hanyoyi ya karu da gina layin dogo da gadoji da makarantu da ma'aikatar makamashi har ma da gina filin jiragen sama da tashar jiragen ruwa.
Yanzu an sabunta hanyar saka jari cikin kasuwancin kasa bisa dokokin da aka tsara. Mun kawar da 'yan baranda da dillalan bogi saboda a taimakawa sahihan masu saka jari ba 'yan wawura ba.
Muna ci gaba da karfafa tattalin arziki tare da rage hauhawan farashi. Muna gina tattalin arzikin da ya rage dogaro ga man fetur. Ta haka muka soma ganin habakar noma duk da ambaliyan ruwan da aka samu".
Da shugaba Buhari ya juya kan matasan Nigeria, ya yaba masu da irin dagewarsu na ganin cewa dimokradiya ta kafu. Ya tabo gwagwarmayarsu a shekarar 1993 lokacin da sojoji suka soke zaben da aka yi. Bai manta da rawar da suka taka ba a zaben shekarar 2015 ba. Ya ce har yau matasanmu na taka mihummiyar rawa a harkokin siyasa tare da ci gaba a fannonin fasaha, noma, hakan ma'adanai, aikin injiniya da nuna kwazo wajen kirkiro abubuwa. "Tare, muna gina tattalin arzikin kasa da zai tabbatar da dogaro ga kai.
Shugaba Buhari yace "cikin shekaru uku da suka gabata mun kaddamar da shirye shiryen karfafa matasa su tsaya daram da kansu. Dalili ke nan da muka goyi bayan dokar da ta rage shekarun takara domin a dama dasu".
Shugaba Buhari ya kira 'yan Nigeria su yi anfani da fasahar zamani domin ci gaban kasa. Ya kira a lura sosai kada a bari a yi anfani da kafofin sadarwa na zamani su zama abun tarwatsa dimokradiyar kasar maimakon karfafa ta,idan kuma ba haka aka yi ba to hakan zai kai ga hasarar dimokradiyar da aka kafa tun shekarar 1999.
Shugaban na Najeriya ya ci gaba da cewa " na yi kokarin tabbatar cewa kowa an bashi damar yin zabe cikin lumana da walwala ba tare da wata tsangwama ba da fatan hukumar zaben kasar za ta kasance mai cikakken 'yanci da gasken gaske. A tuna ta akwatin zabe ne za mu zabi gwamnatin da muke so"
"Yayinda muke bikin tunawa da shekaru 58 da samun 'yanci, duk da cewa muna da banbance banbance mu tuna abubuwan da suka hadamu sun fi yawa. A matsayina na shugaban kasa ina tabbatar maku cewa zan ci gaba da daukaka tare da kare abubuwan da suke da mahimmanci garemu kamar hadin kai, zaman lafiya, tattalin arzikinmu, zaman lafiyar kasa inda kowa zi iya samun nasarar zama duk abun da yake so.
Ga karin bayani cikin rahoton da Umar Farouk Musa ya aiko.
Facebook Forum