Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Ta’dda Sun Yi Awon Gaba Da Mata Sama Da 40 A Wani Sabon Hari Da Aka Kai A Arewa Maso Gabashin Najeriya


Yan Bindiga
Yan Bindiga

'Yan kungiyar IS masu tsattsauran ra'ayi, sun sace akalla mata 42 a wani hari da suka kai a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press a ranar Laraba.

‘Yan ta’addan sun farwa matan ne a lokacin da suke tara itace a gundumar Jere da ke jihar Borno, cibiyar ta’addancin da aka shafe shekaru 14 ana gwabzawa da kungiyar Boko Haram, kamar yadda wani jami’in tsaro na kungiyar tsaron Sa Kai a yankin da ya bayyana kansa da suna Abba ya ce.

Kazalika mazauna yankin sun ce wadanda harin ya rutsa da su sun fito ne daga sansanin ‘yan gudun hijira da ke gundumar Mafa, kuma suna sayar da itacen ne domin bunkasar kudaden shiga yayin da matsalar tattalin arziki a Najeriya ke kara tsananta a karkashin sabon shugaban kasa.

Kachalla Maidugu, mai magana da yawun gwamnati a gundumar, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata amma sai da yammacin Laraba aka samu labarin. Madugu ya ce, “Mun samu labari jiya cewa an sace mata 46, amma hudu ne kawai aka bari su koma gida yayin da aka cigaba da tsare 42.

Ya kuma ce ‘yan ta’addan sun bukaci a biya su kudin fansa naira 50,000 ga kowacce mace ko da shi ke mazauna yankin na tattaunawa kan a rage masu kudaden da za a biya ga matan don a sake su.

Garkuwa da mutane na baya bayan nan da ‘yan ta’addan suka yi ya faru ne sa’o’i bayan da suka yi wa jami’an tsaro da ke kare manoma a yankin kwanton bauna, a cewar Abba.

Kungiyar Boko Haram ta fara tayar da kayar baya ne a shekarar 2009 don yaki da ilimin yammacin duniya da kuma kafa shari'ar Musulunci a Najeriya. Akalla mutane 35,000 ne aka kashe tare da raba mutane miliyan 2.1 da muhallansu sakamakon tashe-tashen hankulan masu tsattsauran ra'ayi, a cewar bayanai daga hukumomin Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya.

~ AP~

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG