Gwamnatin Najeriya, ta tabbatar da kisan wata mata ma’aikaciyar agaji da ‘yan kungiyar Boko Haram su ka kama a farkon wannan shekarar.
Ma’aikatar Yada Labarai ta Najeriya ta bayyana haka a jiya Litinin, inda ta ce an kashe Hauwa Mohammaed Liman, mai aiki a wani asibiti da ke samun tallafi daga kungiyar ba da agaji ta Red Cross.
Hauwa Liman, da Saifura Khorsa, wadanda ke ma kungiyar ICRC aiki, an kama su ne a watan Maris, lokacin da aka kai hari a wani asibiti da ke kauyen Rann a jahar Borno, tare kuma da Alice Loksha, wata jami’ar kiwon lafiya da ke aiki a asibitin da Majalisar Dinkin Duniya ta ke taimaka wa, karkashin shirin UNICEF.
‘Yan ta’addar ISIS ne tare da hadin gwiwar ‘yan Boko Haram su ka kama matan. Ma'ikatar Yada labaran ta kara da cewar gwamnati ta yi bakin kokarinta na ganin ta daidaita da ‘yan ta’addar don ceto rayuwar Hauwa.
Facebook Forum