Shaidu a Guinea sun ce akala mutane biyu sun mutu a wata fafatawar da aka yi tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar kyamar gwamnati.
Fadan ya barke ne a yau Talata a Conakry, babban birnin kasar bayan day an sanda da jami’an tsaron Majalisar su ka hana magoya bayan ‘yan adawar yin gangami. Shugabannin ‘yan adawar sun kira zanga-zangar ce don su nuna rashin amincewarsu da yadda gwamnati ke tafi da shirin zaben majalisar da ke gabatowa.
Shaidu sun ce jami’an tsaro sun yi ta harba barkwanon tsohuwa tare da amfani da kulake don tarwatsa masu zanga-zangar, wadanda wasunsu kuma ke jifa da duwatsu.
Gamayyar kungiyoyin adawa sun zargi shugaba Alpha Conde da yinkurin yin magudi don ya yi galaba a zaben. Ana sa ran gudanar da zaben zuwa karshen wannan shekarar.
Mr. Conde ya hau karagar mulki cikin watan Disamba bayan ya ci zaben Guinea na farko na dimokaradiyya tun bayan da kasar ta sami ‘yanci a 1958.