Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sanda A Jihar Kros Riba Na Samun Nasarar Dakile Miyagun Laifuka - Kwamishina


Rundunar yan sanda.
Rundunar yan sanda.

Yayin da hukumomi na ci gaba da inganta dabaru wajen samar da maslaha ga matsalar tsaro da kasar ke fama da ita, ‘yan sanda dai a jihar Kros Riba da ke kudu maso kudancin Najeriya sun ce suna samun gagarumar nasara akan miyagun laifuka a fadin jihar.

Kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar Malam Aminu Alhassan ne ya shaida wa Muryar Amurka hakan a wata hira, inda ya karkare da cewa kalubalolin da ‘yan sanda ke fuskanta a jihar yanzu ‘yan kalilan ne, kamar batun ayyukan masu fafutukar kafa kasashen Biafra da Ambazonia, da kuma batun masu safarar makamai.

Sai dai Malam Musa Kutama wani mai fashin baki kan lamuran yau da kullum da kuma mazaunin Calabar, babban birnin jihar Kros Riban, ya ce duk da cewa ana samun nasarar, har yanzu akwai bukatar kara inganta tsaro a wuraren shakatawa da makarantu da wuraren kasuwanci, da kuma sauran wuraren walwala.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:37 0:00

XS
SM
MD
LG