Wata tashar talibijan ta nan Amurka, wato CNN, ta fara fallasa batun sayar da mutane a matsayin bayi a Libya inda ta ga yadda aka yi cinikin wani dan Najeriya akan kudi dalar Amurka dari hudu.
Bayan labarin na CNN kasashe irin su Najeriya , Niger da Kamaru sun shiga jigilar dawo da mutanensu daga Libya ta hanyar aikawa da jirage.
Kawo yanzu, kamar yadda hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya ta shaida, mutane fiye da dubu biyar ne suka dawo daga Libya kuma kusan kowannensu na da labarin ukubar da ya sha.
Mutane irinsu Ewere Joseph, Alex Otoide (Vanguard December 17, 2017) sun shaida ganin yadda 'yan Najeriya ke sayar da 'yan kasar wa wasu 'yan Najeriyan dake zaune a kasar ta Libya. Bayan sun sayesu, su ma sai su sayarwa Larabawan Libyan wadanda ke sa mazan yin aikin bauta a gonakansu ko masana'antansu. Mata kuma sai su zama abun yin lalata dasu a hannun wadanda suka sayesu. Ta hakan da dama suka yi ciki har suka haihu. Dalili ke nan da wasunsu suka isa Najeriya da yara kanana ko jarirai.
Rahotanni sun nuna cewa da yawa sun rasa rayukansu a gidajen yari. A cewar wasu ganao jami'an tsaro kan kai samame gonaki ko masana'antu su kama duk wanda bashi da takardar zama kasar. 'Yan Najeriya da dama da suke aikin bauta suka fada hannun hukumomin kasar.
Duk wanda ya shiga gidan yari duka shike sha dare da rana idan bai iya biyan tarar da aka dora masa ba. Sau tari ba sa iya biyan tarar . Ta hakan da yawa sun rasa rayukansu saboda tsananin duka tare da hanasu abinci.
Facebook Forum