ABUJA, NIGERIA - Da yake karin bayani akan batun, daraktan cibiyar tattara bayanai kan arangamar da dakarun kasar ke yi, Manjo Janar Bernard Onyeako ya ce adadin ya hada da mata dubu daya da dari hudu da goma sha biyar, yara dubu biyu da dari hudu da cas'in, da manza manya su dari takwas da sittin da hudu.
Janar Onyeako ya ce matsin lambar da ‘yan ta'addan ke fuskanta ne babban dalilin da ya sa suke ta mika wuya akai akai domin basu da zabi illa su mika wuya, kasancewar sojoji sun rushe sansanoninsu.
Wasu daga cikin mayakan na Boko Haram da suka mika wuya sun koka kan irin kuncin rayuwar da suka sha fama da ita a cikin daji, al'amarin da suka ce abin nadama ne matuka.
Masana harkar tsaro irinsu Dr. Yahuza Ahmed Getso, na ganin wannan dama ce ga gwamnati da jami'an tsaro ta samun muhimman bayanai daga wadanda suka ajiye makaman tare da mika wuya akan ainihin tsarin kungiyar da kuma masu daukar nauyinta.
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina: