Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kato da Gora Na Fatan Zasu Zama Sojoji Bayan An Murkushe Boko Haram


‘Yan kato da gora, da mafarauta na amfani da bindigogin gargajiya wajen yin sintiri
‘Yan kato da gora, da mafarauta na amfani da bindigogin gargajiya wajen yin sintiri

‘Yan kato da gora dake arewa maso gabashin Najeriya sun taka rawar gani wajen yaki da kungiyar Boko Haram.

Da yake yanzu an sha karfin kungiyar ta Boko Haram, wadannan ‘yan kato da gora suna fatan ganin an dauke su aikin tsaro masu sa kayan sarki.

Jihar Borno dake cikin tarayyar Najeriya dai, nan ne Boko Haram ta kwashe shekaru da dama tana ta'adanci, kuma wannan kungiyar ta ‘yan kato da gora ta taka rawar ganin an kakkabesu.

CIVILIAN JTF, YAN KATO DA GORA
CIVILIAN JTF, YAN KATO DA GORA

Wadannan ‘yan kungiyar mazan su da matan, sun taimakawa jamia'an tsaro domin kare al’ummar su kana sun samu nasarar kame dubban ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun mika su ga jamia'an tsaron kasar, haka kuma suna baiwa sojojin bayanai masu muhimmaci da suka iya agaza musu wajen yaki da kungiyar.

Wasu ma cewa suka yi ‘yan kungiyar ta Boko Haram sunfi shakkar ‘yan kato da gora fiye da sojojin kasar.

Sai dai kungiyar ta Boko Haram a ramuwar gayya inda tayi ta wa mutane da yawa kisa tare da kone kauyuka, kana su na gargadin mutane su daina hada kai da gwamnati.

Yanzu haka sojojin Najeriya da na hadin gwiwa daga kasashen makwabta sun karya lagon kugiyar ta Boko Haram

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG