Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Kasar Cameroon Dake Zaune Kasashen Waje Sun Amsa Kira.


'Yan gudun hijirar da Boko Haram ta rabasu da gidajen su
'Yan gudun hijirar da Boko Haram ta rabasu da gidajen su

Gwamnatin kasar Cameroon ta yi kra ga ‘yan kasar dake kasar waje dasu dawo gida domin kafa masanaantu.

Gwamnatin tace zata rage musu haraji kuma zata basu tallafin da duk suke bukata domin yin hakan zai samar da aikin yi cikin kasa.

Hajiya Fatima na daya daga cikin ire-iren wadannan mutanen da ta dawo daga kasar Faransa, kuma wakilin Muryar Amurka Awal Garba ya tambaye ta kome ya bata sha’awa ta amsa wannan kiran?

‘’Wato abinda ya bani shaawar dawo gida kasar Cameroon bude kanfanin sarrafa ruwan sha shine domin na taimaka wa ‘yan uwa na na kasar Cameroon, haka ita ma gwamnati ta dafa muna kan wannan kudiri namu, tace daga shekaru biyu zuwa biyar zasu rage muna haraji’’.

Malama Aisha ita ma daga kasar Hadaddiyar Daular Larabawa wato (Dubai) da niyyar bude maaikatar dinkin hannu, kamar zanin gado da kuma kujerun daki.

‘’Ina son in taimakawa kasa ta nima inga taci gaba kuma gashi ance za ayi muna ragin haraji hakan kuma zai taimakawa matasa su samu aiki’’

Ga Muhamma Awal Garba da Karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG