Dubban mutane daga Kaduna su ka yi sammako zuwa kasuwanni da bankuna don tanadin kayan bukatu da kudin kashewa biyo bayan dage dokar hana zirga-zirga a jihar na yini biyu wanda ya kare a daren jiya Alhamis.
An dai samu cunkoson mutane da ababen hawa a kasuwanni da bankuna a Kaduna amma duk da haka wasu sun ce bukata dai bata biya ba, kuma har lokacin da gwamnati ta bayar ya kare.
Tsohon shugaban kananan 'yan kasuwa reshen Kawo, Alh. Shehu Mohd Mai-gona Gulma ya ce duk da sassauta dokar hana zirga-zirgar, kanan 'yan-kasuwa na cikin wani hali.
Ya ce “idan aka ce a rufe kasuwanni, yadda mutane suke cikin yunwa da talauci, gaskiya babu adalci a ciki.”
Gwamnatin Kaduna dai ta ce an yi wannan sassauci ne don al'umma su sami sauki, inji kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Malam Samuel Aruwan.
Tun a daren jiya dai kowa ya koma gida kamar yadda gwamnatin jihar Kaduna ta bada umurni sai kuma makon gobe gwamnatin ta ce za ta kara sassauta dokar a ranakun Talata da Laraba idan ba'a sami wata matsala ba.
Facebook Forum