Babbar jam'iyyar hamayya a Afirka tana shirin ta kalubalanci shawarar da gwamnatin kasar ta yanke na janyewa kasar daga kotun kasa da kasa mai hukunta manyan laifuffukan-yaki dake Haque. Jam'iyyar Democratic Allaince da turanci (DA) a takaice, tace zata tafi kotun tsarin mulki ranar Litinin, domin daukar wannan mataki.
Wannan yana zuwa ne bayan da ministan shariya na kasar Michael Musutha, yace gwamnatin zata gabatar kuduri ga 'yan majalisar kasar domin su amince da janyewa daga kotun, wacce Afirka ta kudu ta rattaba hanu kan dokar da ta kafata a a wani taro da aka yi a Roma.
A ranar jumma'a ce Afirka ta kudu ta shaidawa MDDa hukumance cewa zata janye daga kotun.
Amma dan majalisa dokokin kasar, James Selfe, jigo cikin wakilai karkashin jam'iyyar DA mai hamayya, yace gwamnatin shugaba Zuma ta sabawa tsarin mulki data gayawa MDD, gabannin ta sami amincewar majalisar dokokin kasar.
Shawarar Afirka ta kudu na shirin janyewa daga kotun yazo ne kwanaki bayan da majalisar dokokin kasar Burundi ta amince da kudurin hukumomin kasar dake Bujumbura fadar gwamnati na janyewa daga kotun duniyar mai cibiya a birnin Haque.
Kungiyar hada kan kasashen Afirka tana sukar kotun ta kasa da kasa. Kungiyar tace kotun tafi auna 'yan Afirka,alhali ga keta 'yancin BIl'Adama da cin zarafin jama'a ta ko ina afadin duniya.
Ahalin da ake ciki kuma, wata kotu a Acrra babban birnin kasar Ghana zata fara bin bahasin kararda 'yan hamayya 12 a Ghana suka shigar na kalubale ga matakin da hukumar zaben kasar ta dauka na hanasu yin takara. Cikinsu har da uwargidan tsohon shugaba kasar Nana Konadu Rawlings ta jam'iyyar NDP.