Kawo yanzu mutane fiye da dubu biyu da dari hudu ne suka kwarara cikin Jamhuriyar Nijar daga jihohin Borno da Adamawa da Yobe saboda da dokar ta baci da gwamnatin Najeriya ta saka wa jihohin.
Yunkurin Kakkabe 'yan bindiga da sojoji ke yi ya tsorata mutane, don haka ne suka arce daga gidajensu. Yawancin wadanda suka nemi mafaka a Nijar mata ne da yara.
Akwai rahoton dake cewa wasu na shiga Najeriya da safe kana da yamma su koma Nijar.
Rahotanni da Muryar Amurka ya samu sun ce an ga jerin gwanon motoci da kayan agaji akan hanyarsu zuwa wadanda ke gudun hijirar.
Hukumomin Nijar sun ce yawanci 'yan gudun hijiran, Filani da Barebari, suna zaune ne da yan’uwa wato babu wani sansani na musamman na 'yan gudun hijirar.
Abdullahi Maman Ahmadu na da karin bayani a wannan rahoton.