Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan fashin teku sun yi fashi a wani jirgin dake gabar tekun Najeriya


Jirgen ruwa a cikin teku
Jirgen ruwa a cikin teku

Kungiyar sa ido kan harkokin jiragen ruwa tace ‘yan fashin teku sun yi garkuwa da wasu matukan wani jirgin dako da ya tsaya kusa da gabar Nijeriya.

Wata kungiyar sa ido kan harkokin jiragen ruwa ta fadi yau Laraba cewa ‘yan fashin teku sun yi garkuwa da akalla biyu daga cikin matukan wani jirgin dako da ya tsaya kusa da gabar Nijeriya.

Kungiyar Kula da Harkokin Jiragen ruwa ta kasa da kasa, ta ce mafasan ruwan ‘yan Nijeriya su 8 sun bude wuta kan wani jirgin ruwa mallakar wani kamfanin Dutch a jiya Talata, suka yiwa mutane 14 da ke cikin jirgin fashi sannan suka tsere cikin wani dan karamin jirgi mai gudun tsiya da Kaftin din jirgin da Injiniya.

Kungiyar ta ce wani daga cikin matuka jirgin ya bace wani kuma ya sami wasu raunukan da ba a bayyana ba sanadiyyar wannan harin.

‘Yan fashin tekun na mashigar ruwan Guinea suna fashi gabansu gadi cikin ‘yan watannin nan. Kungiyar ta IMB ta ce an sami rahoton fashin taku har sau 7 a wannan yankin cikin shekarar nan.

XS
SM
MD
LG