Rahotanni daga jihar Benue da tsakiyar arewacin Najeriya na cewa, wasu ‘yan bindiga sun sace daliban da ba a san adadinsu ba a jami’ar nazarin aikin noma ta tarraya.
Hukumomin jami’ar, wacce ke Makurdi, babban birnin jihar ne suka sanar da sace daliban a ranar Litinin.
Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito wata sanarwa da jami’ar ta fitar dauke da sa hannun Darektar yada labarai Mrs Rosemary Waku, wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin.
“Ba mu ji komai daga daliban ko wadanda suka yi garkuwa da su ba, tun bayan aukuwar lamarin.” Sanawar ta ce.
Rahotannin sun ce a daren Lahadi ‘yan bindigar suka shiga jami’ar suka yi awon gaba da daliban bayan da suka yi musu barazana da makaman da ke hannunsu.
Wannan lamari na faruwa ne kasa da mako guda bayan da aka sace daliban jami’ar Greenfield da ke jihar Kaduna.
Greenfield, jami’a ce mai zaman kanta wacce ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.
A karshen makon da ya gabata aka tsinci gawarwakin uku daga cikin daliban jami'ar ta Greenfield, kamar yadda hukumomin jihar ta Kaduna suka tabbatar.