Wasu ‘yan fashin daji da ba’a san ko su wane ne ba, sun kai wani mummunan hari a wani wurin hakar ma’adanan karkashin kasa a jihar Nejan da ke tsakiyar arewacin Najeriya.
Rahotanni daga yankin sun tabbatar da cewa harin ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an tsaro da dama da kuma farar hula.
Kazalika sun yi garkuwa da wasu ‘yan kasar China guda hudu kamar yadda rahotanni ke nunawa.
Lamarin dai da ya faru ne a kauyen Ajata Aboki da ke yankin karamar hukumar Shiroro a cikin daren Laraba wayewar garin Alhamis.
Harin ya yi matukar jefa mazauna yankin cikin wani yanayi na tashin hankali a cewar tsohon Shugaban karamar Hukumar ta shiroro ASP Abdullahi Yarima Mai Ritaya.
Gwamnatin jihar Nejan ta tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai kwamishinan kula da harkokin tsaro da walwalar jama’a a jihar Nejan Mr. Emmanuel Umar, ya ce kawo yanzu ba su tantance iya adadin wadanda aka kashe ba.
Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto dai babu wani karin haske daga rundunar ‘yan sanda ta jihar Nejan akan wannan sabon hari, domin kuwa kokarin samun kakakin ‘yansanda Wasiu Abiodun da ma Kwamishinnan ‘yan sandan ya ci tura.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari daga Minna: