Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan bindigar da suka kaddamar da hare-hare kan wasu majami’u guda 2 dake kauyen Bakinpah-Maro a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, sun kashe akalla mutane 3 tare da yin awon gaba da wasu da dama.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewar, al’amarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadin data gabata sa’ilin da gungun ‘yan bindiga masu tarin yawa suka mamaye majami’ar ECWA data katolika dake kauyen ana tsaka da gudanar da ibada.
A cewar tsohon shugaban karamar hukumar Kajuru, Cafro Caino, ‘yan bindigar sun yi awon gaba da mutane 30 daga majami’un 2 ciki harda wani fasto, Bernard Gajera.
Da yake tabbatarwa da tashar talabijin ta Channels da afkuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda ta Kaduna, ASP Mansur Hassan, yace ‘yan bindigar sun hallaka mutane 3.
Kakakin rundunar ‘yan sandan yace har yanzu ba’a kai ga tantance adadin mutanen da aka yi garkuwa dasu din ba.
Sai dai, yace ‘yan sanda da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro sun kaddamar da aikin farautar ‘yan bindigar domin kamosu tare da kubutar da mutanen da suka sace.
Dandalin Mu Tattauna