Demokuradiyyar Kwango, rahotanni daga kamfanin dillancin Labarai na Reuters, ya ruwaito cewa mayakan sakai sun kai harin kwanton bauna kan farar hula su kamar 30 a arewa maso gabashin kasar, suka kashe da dama daga cikinsu, kamin daga bisani suka gwabza kazamin fada da sojojin kasar, kamar yadda aka ji daga bakin 'yan siyasa.
An kai harin ne kusa da birnin da ake kira Beni, kuma idan har aka tabbatar da yawan mutanen d a aka kashe sakamakon harin,wannan zai kasance karon farko da a bana d a za'a kashe mutane a wannan yanki. An sami zaman lafiya a yankin tun bayan da aka kashe mutane fiyeda 800, a wasu hare hare munana tsakanin shekara ta 2014-2016.
Wadannan hare hare sun jefa ayar tanbaya ko gwamnatin kasar tana da karfin ta tabbatar da doka da oda a yankin da yake fama da zaman dar dar tsakanin kabilu da kuma bata gari wadanda suke kokarin amfana daga albarkatun kasa d a Allah Ya zuba yankin.
Facebook Forum