Fursunoni akalla 118 ne suka tsere daga wani gidan kurkukun gwamnatin tarayyar Najeriya, a bayan da wasu 'yan bindiga suka tarwatsa kofar shiga ciki da bam, suka kuma kashe ganduroba guda daya a harbe-harben da aka yi ta yi daga baya.
Wannan gidan kurkuku yana garin Koton-Karfe, a Jihar Kogi, kimanin kilomita 120 a kudu maso yamma da Abuja, babban birnin kasar. 'Yan sanda suka ce wadannan 'yan bindiga sun fasa gidan kurkukun ne jiya laraba da daddare.
Shaidu sun ce ‘yan bindiga su kimanin 20 a kan babura sun kai farmaki a kan gidan kurkukun tarayya dake garin Koton Karfe na jihar Kogi, jiya laraba da maraice, suka yi harbi kan gandurobobin dake gadin gidan, kafin su tayar da bam a babbar kofar shiga ciki. Shaidu suka ce an kashe ganduroba guda daya, yayin da sauran suka gudu a lokacin wannan ba-ta-kashi.
Rahotanni daga yankin dake kudu da Abuja, babban birnin kasar, sun ce ‘ya’yan kungiyar nan ce ta Boko Haram suka kai farmakin. Shaidun suka ce ‘yan bindigar sun kubutar da ‘ya’yan wannan kungiya ce, yayin da sauran fursunoni kuma suka sulale suka gudu a lokacin wannan yamutsin.
A jiya larabar kuma, hukumomin Najeriya sun ayyana cewa su na neman wani tsohon soja ruwa a jallo dangane da harin da aka kai kan wata majami’a ranar kirsimeti, aka kashe mutane da dama a kusa da Abuja.
An ce tsohon sojan mai suna Habibu Bama, ya hada baki tare da Kabiru Sokoto wanda aka sake kamowa a makon da ya shige bayan da ya kwace daga hannun ‘yan sanda tare da taimakon kungiyar Boko Haram.