A rahoton da wakilin muryar Amurka Ibrahim Abdulaziz ya aikowa muryar Amurka na cewa harbe-harben ‘yan bindigar ya raunata mutane da dama. ‘Yan bindigar suna kan babura ne lokacin da suka bude wuta a daidai lokacin da suka isa cunkoson jama’a dake hada-hadar cinikayya kuma ba nisa da shalkwatar rundunar ‘yan sandan Nigeria dake Yola.
Hakan ba shine karo na farko da ake samun ‘yan bindigar suna kai hare-hare kan jama’a ba a jihar Adamwa, abinda ya janyo hankulan shugabannin al’umma suke kira ga jami’an tsaro da su karfafa daukan matakan tsaro ciki da wajen birnin Yola. Amma ana kyautata cewar ‘yan bindigar basa rasa nasaba da kungiyar Boko Haram.