Alhaji Ahmed Lawal sakataren tsare-tsare na jam'iyyar a jihar ya bayyana dalilansu na wannan korafin da suke yi.
A cewarsa ba'a tuntubesu ba a jam'iyyance kafin a zabi wanda aka fitar da sunansa.Yace ya kamata duk abun da za'a yi a nemi shawarar jam'iyya. Idan za'a bada mukami yakamata a dubi wadanda suka yiwa jam'iyyar fafutika har ta kaiga kafa gwamnati.
Alhaji Ahmed Lawal yace wanda aka dauko a ba minista su har ga Allah basu sanshi ba. Ba mutane wadanda basu yiwa jam'iyya komi ba mukami shi zai kawowa jam'iyyar matsala a zaben 2019 mai zuwa, inji Alhaji Lawal.
Shi ma wani kusa a jam'iyyar Dr. Umar Duhu tsohon shugaban jam'iyyar a yankin arewa maso gabas yace akwai bukatar a sake nazari akan ministan da aka dauko daga jihar Adamawa. Yakamata a yi tafiya tare domin zabe mai zuwa. Idan ba'a yi ba su 'yan siyasa zasu koma gefe daya suna kallo. Kafin a yi nisa ya dace shugaba Buhari ya yi gyara domin Muhammad Bello da ya dauko daga jihar Adamawa ba dan siyasa ba ne.
To saidai 'yan tsohuwar hukumar alhazan jihar Adamawa daga inda aka zakulo Muhammad Bello sun yabawa shugaba Buhari da zabarsa. Alhaji Aminu Iyawa tsohon kwamishana a zamanin mulkin Nyako yace zaben Muhammad Bello ba sai an tuntubesu ba saboda ya dace. Yace shugaba Buhari ya ba dan siyasa daga jihar mukamin sakataren gwamnati saboda haka ba jihar mukamin minista kuma kamar garabasa ce.
Ga karin bayani.