Kundun tsarin mulkin kasar Nijar ya dorawa hukumar kula da hakokin sadarwa ko CSC a takaice alhakin tabbatar da cewa kowa ya samu shiga kafofin labarai mallakar gwamnati ba tare da nuna fifiko ba.
Kundun tsarin mulkin ya yiwa kowa tanadi. Duk jam'iyyun kasar ko na gwamnati ko na adawa suna da lokaci daidai da juna su yi anfani da kafofin labarai mallakar gwamnati.
Amma duk da wannan tanadi 'yan adawa na korafe korafe cewa ba'a basu dama kamar yadda doka ta tanada ba. Bugu da kari an zargi jam'iyyun dake mulki cewa basa ba 'yan adawa dama daidai gwargwado. Mai makon haka ma jam'iyyun gwamnati suna cin karensu ba bababbaka.
Taron da hukumar sadarwa ko CSC ta shirya yana da manufar magance irin wadannan korafe - korafen. Za'a yi kokarin kawar da duk abubuwan dake hana 'yan adawa shiga kafofin labarai mallakar gwamnati. Malam Hassan Sale wakilin jam'iyyun adawa sun ce kafofin labaran gwamnati basa yadda da 'yan adawa. Idan an tambayesu sai su ce umurni suka samu daga sama.
Malam Abdulrahaman Usman shugaban hukumar dake tace labarai ta kasa ko CSC a takaice yace idan wata jam'iyyar siyasa da hukumarsa ta ki ta karbi labaransu su fito su bayyana lamarin.
Saidai bangaren jam'iyyun gwamnati suna ganin rashin abun fada ne da kawai. A zahiri ma su 'yan adawan suke jawo ma kansu kamar yadda kakakin jam'iyyun dake mulki ya sahaida.
Ga rahoton Abdullahi Manman Ahmadu.