A cewar Yakubu Musa Ahmad, gwamnatin ba ta tafi da matasa ba a wancan mulkin na ta na farko da ta yi a jihar Kano, hakan dai ya sa matasa suka nunawa gwamnatin jihar muhimmanci ta hanyar kin amincewa da kudirin da ta zo da shi na sake mulki a karo na biyu.
Nuna tirjiya da matasa suka yi ya ja hankalin gwamnatin wajen sanin muhimmanci su a don haka ne ma matasa a wannan sabuwar gwamnati ke tsammani samun canji na yadda ake tafiyar da mulki ba tare da barin matasa a baya ba.
Ya ce sun yi korafe-korafai a wancan lokaci ganin cewar matasa su ne ginshikin kowacce al’umma a harka na ci gaban kasa, a don haka ne suke fatan a wannan karo su ka bukaci san matsalolin matasa da yadda za’a magance musu matsalolin na su.
Ya kara da cewa abin takaici ne yadda ake baiwa matasa wasu kayan da basu taka kara sun karya ba da zummar an baiwa matasa jari ko kayan da zasu kama sana’a da shi.
Daga karshe ya ja hankali matasa da su jajirce wajen neman na kansu da tabbatar da an dama da su a mulki na demokradiya.
Facebook Forum