Ikirarin samun nasarar yaki da boko haram da mahukuntar jamhuriyar Niger keyi ba sabon labari bane a cikin kasar.
Wannan ikirarin daga matakin koli har na zuwa yankin Diffa wanda yafi fuskantar hukubar wannan yaki wanda ya tilasta jamaa barin matsugunnin su, zuwa wasu wurare har yanzu akwai sauran sa.
Shugaban karkaran Diffa, Alhaji Mahiru Ligali ya shaidawa wakilin sashen Hausa na muryar Amurka cewa duk mutumin da kake yaki dashi baka ganin sa akwai hadari.
Yace gaba daya a kasar Diffa ba inda zaka je ka taras da taron jamaa kace wadannan ‘yan boko haram ne, don haka yace da sauran rina a kaba.
Harin da ‘yan kungiyar suka kai a ranar 17 ga watan janairu a garin Tumur wanda yayi dalilin mutuwar jamian tsaro7 kuma ya haifar da mutuwar sojoji biyu ya nuna cewa har yanzu boko haram basu kau ba.
Ga Sule Mummuni Barma da Karin bayani
Facebook Forum