Babban hafsan mayakan sama a Najeriya Air Marshall Sadiq Abubakar ya ziyarci Sokoto, domin nazarin abın da ya kamata a yi kan hare-haren da ake yawan kai wa a Sokoto.
A karshen makon da ya gabata ne ya kai ziyarar kuma daga isa jihar ya fara zuwa gidan sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar na uku ne domin fara tattaunawa da shi.
A cewar Air Marshall Sadiq, "wannan aiki na samar da zaman lafiya, aiki ne da muka riga muka fara a Zamfara da Katsina, yanzu kuma za mu soma shi ne a Sokoto."
Mai alfarma Sarkin Musulmin dai ya yi na'am da wannan matakin, kuma ya ce idan aka samar da kayan aiki, tabbas za a fi karfin 'yan ta'addan.
A cewar wata tawagar da aka nada domin gano yawan mutanen da suka rasa rayukansu a hare-haren kwannakin nan kadai, mutanen sun kusan kai 100.
Ko a karshen makon da ya gabata dai sai da aka sake kai wani hari a kauyen Gatawa wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka biyu, aka kuma sace wasu mutum biyu.
Facebook Forum