Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda ‘Yan Sanda Suka Amfana Da Zanga Zangar #EndSars


Wasu matasa sun yi zanga-zangar bukatar kawo karshen SARS a gaban ginin shelkwatar ‘yan sanda da ke Abuja, Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:51 0:00

Wasu matasa sun yi zanga-zangar bukatar kawo karshen SARS a gaban ginin shelkwatar ‘yan sanda da ke Abuja, Najeriya, Oktoba 9, 2020.

Gwamnatin Najeriya ta karawa jami’an ‘yan sanda albashi da kashi 20% da zai fara aiki daga watan Janairu na 2022.

Hakan na daga cikin bukatu 5 da masu zanga zangar ENDSARS su ka gabatarwa gwamnati.

Ministan ‘yan sanda Muhammad Maigari Dingyadi ne ya bayyana haka bayan taron majalisar zartarwa na Ranar Larabar nan.

Dingyadi ya ce wannan yunkuri da aka yi na daya daga cikin bukatu 5 da masu zanga-zangar ENDSARS su ka gabatarwa gwamnati.

Zanga Zangar #ENDSARS
Zanga Zangar #ENDSARS

Ministan na ’Yan Sanda ya ce za a yi karin ne ta hanyar dada musu kudaden alawus-alawus dinsu da kaso shida cikin 100, da kuma karin Naira biliyan 1.1 don biyan basussukan da suke bi na tsakanin shekarar 2013 zuwa 2020.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda shi ne ya jagoranci taron, ya ce za a kara albashin ne don ya dace da ayyukan da suke yi da kuma karfafa yunkurin samar da zaman lafiya a kasa.

'Yan Sanda A Jihar Zamfara
'Yan Sanda A Jihar Zamfara

Wannan ya nuna duk jami’an ‘yan sanda a fadin kasar za su samu karin akalla kashi 20% na albashin da su ke karba a yanzu.

Ba mamaki wannan ya rage korafin ‘yan sandan na rashin ingancin albashi da ma kudin fansho bayan ritaya daga aiki.

kwamitin-duba-zargin-cin-zarrafi-da-kisan-gillan-masu-zanga-zangar-endsars-a-lekki-ya-saba-ka-ida---keyamo

rahoton-endsars-wata-karyar-ce-kawai-aka-tsara-inji-gwamnatin-najeriya

wasu-sojojin-najeriya-sun-tsare-ma-aikaciyar-voa-a-port-harcourt

Ministan 'Yan Sanda Muhammad Maigari Dingyadi
Ministan 'Yan Sanda Muhammad Maigari Dingyadi

Masu kula da lamura na kuma kyautata zaton karin albashin zai rage cin hanci da rashawa da ake zargin wadansu jami'an 'yan sanda da aikatawa da ake dangantawa da rashin kyaun tsarin kula da 'yan sanda.

Bayan zanga zangar da aka gudaar a birane da dama na Najeriya da ya sami asali daga gangamin da matasa su ka fara a birnin Lagos na neman kawo karshen gallazawa al'umma da jami'an 'yan sanda su ke yi da kuma neman kudi da karfi da yaji a hannun wadanda su ka kama, matasan sun ba gwamnati zabi kan matakan da za a dauka kafin su daina zanga zanga da suka hada da karawa jami'an 'yan sanda albashi da kuma daukar matakan mutunta aikin da inganta rayuwarsu.

Zanga Zangar #ENDSARS
Zanga Zangar #ENDSARS

sars-tsabar-azaba-ta-sa-ni-amsa-laifin-da-ban-aikata-ba

ana-zargin-wani-dpo-da-azabtar-da-mutane-da-tabarya-a-bauchi

endsars-sojoji-sun-bada-bahasi-gaban-kwamitin-bincike

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG