À ƙarshen wasa tsakanin Kamaru da Comoros, mutun 8 daga cikin' yan kallo sun rasa rayukan su, inda wasu da dama suka jikkata a sanadiyar cunkoso da aka samu wajen fitowa daga filin wasa.
Wadanda suka raunana, an kai su asibitin Messassi da ya fi kusa da filin wasan Olembe.
À fannin wasa, Kamaru ta tabbatar da kasancewar ta ɗaya daga cikin ƙasashen da ake yi wa zaton cin kofin Afirka na bana. Indomitables Lions sun doke Comoros ci 2-1.
Lamba 12 Kamaru mai suna Karl Toko Ekambi ne ya bude raga a mintuna 29 da fara wasa. Sa'annan Kaftan Vincent Aboubakarya wanda ya fi cin kwallaye ya zura ƙwallo daya a mintuna 70.
Duk da haka 'yan wasan Comoros ba su yi ƙasa a gwiwa ba. A mintuna 80, Youssouf M'Changama mai ɗauke da lamba 10 ya zura kyakkyawan ƙwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida. Amma hakan bai hana yan Kamaru zuwa kwata fainal ba, inda za su keta raini da Gambiya a ranar Asabar mai zuwa a birnin Douala.
Abin sani anan shi ne 'yan Comoros sun ƙarasa wannan wasa da mutun goma mai makon 11 a sanadiyar jan kati da aka bai wa Nadjim Abdou, a mintuna 7 da fara wasa.