Kamar yadda binciken likitoci suka tabbatar an fi samu wannan matsalar ta saran macizai a irin wannan lokaci na damuna, wanda kuma gwamnatoci a wasu jihohi kan fitar da wani tsari na samar da magungunan saran macizai kyauta.
Sai dai a jihar Adamawa da ke da yawan manoma, tsadar maganin kashe dafin maciji na sa majinyata wanda macizi ya sare su, kauracewa asibitocin gwamnatin jihar inda suka koma na gargajiya.
Tsadar maganin dai ya yi tashin goron zabi inda ko wane sha, ko allura guda ake saya akan naira 40,000, a cewar wani dan uwan wani da aka kwantar a asibitin kwararru da ke Yola, wato Yola Specialist hospital.
Wakilin Muryar Amurka ya yi kokarin jin ta bakin bakin ma'aikatan kiwon lafiya na jihar amma haka ba ta cimma ruwa ba.
Sai dai kuma, jami'in hulda da jama'a na asibitin kwararru Mr. Ezekiel Mathias ya danganta karancin maganin da kuma tsadar sa ga annobar cutar Coronavirus.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum