Ranar 3 ga watan Mayun kowacce shekara rana ce na tunatar da gwamnatoci bukatar mutunta alkawuran da suka dauka game da 'yancin 'yan jaridu kuma rana ce na yin nazari tsakanin fitattun 'yan jarida a kan batutuwan da suka shafi 'yancinsu tare da yin aiki da ka’idoji da kuma kwarewa.
Tun ba yau ba, yan jarida ke fuskantar barazana a lokutan da suke tsakar aikinsu kuma su ke da alhakin tabbatar da cewa al’umma a fadin duniya sun samu sahihan labarai.
A halin da duniya ke ciki yanzu kan cutar Coronavirus (koronabairus), yan jarida na dada fuskantar barazana wajen gudanar da ayyukansu.
A Najeriya, Babban sakatare kungiyar 'yan jaridar kasar wato NUJ, Shu’aibu Usman Leman, ya bayyana cewa a yau da kullum ‘yan jaridu na fuskantar kalubale ta fuskar aiki, albashi, da ma kayan aiki.
A nata bangaren, wata fitacciyar ‘yar jarida da ta shafe sama da shekaru ashirin a kan aikin, Hajiya Halima Tahir, ta yi tsokaci a kan halin da yan jaridu ke ciki na rashin 'yancin gudanar da ayyukansu musamman a wasu kasashe, da kuma yadda tashe-tashen hankula kan rutsa da su.
Rashin kwarewar aiki na daya daga cikin kalubalen da ke saka aikin cikin shakku, inda Ibrahim Inuwa Addra, fitaccen dan jarida ya ce ana bukatar karin horo ga 'yan jarida a Najeriya.
Kamar yadda wannan rana ke da mahinmanci a duniya, kafaffen yada labarai na bukatar tallafi daga gwamnatoci wajen kare 'yancinsu da kuma taimaka wa iyalan 'yan jarida da suka rasa rayukansu a yayin aikin neman labarai.
Ga Halima Abdulrauf da cikakken rahoton:
Facebook Forum