Bayan shafe kimanin wata uku a cikin dokar kulle, domin kare al’umma daga kamuwa ko yada annobar COVID-19, hukumomi a jihar Kano sun dage dokar domin baiwa al’umma damar gudanar da harkokin na yau da kullum kamar yadda aka saba.
Ya zuwa yanzu dai mazauna birnin da kewayen jihar Kano na cike da farin ciki game da wannan mataki da gwamnati ta dauka.
Ko da yake, an sassauta dokar bayan sanya ta da kimanin wata biyu, amma a jiya ne gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da janye dokar baki dayanta, saboda abin da ya kira kyautatuwar yanayi game da yaki da cutar ta coronavirus.
Sai dai gwamnatin jihar ta gindaya wasu sharruda.
Malam Abba Anwar da ke zaman sakataren labarai na gwamnan Kano ya yi Karin bayani game da wannan batu, inda ya ce, za a bude kasuwanni da tashoshin motoci, amma dole ne jama’a su saka takunkumin rufe fuska tare da tsaftace hannu a koda yaushe.
Su ma dai mazauna birnin Kano sun bayyana gamsuwa game da wannan mataki na janye dokar kulle a Kano.
Wannan ci gaba dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke dakon gwamnatin kasar ta sanar da lokacin da za a bude makarantu domin ci gaba da daukar darrusa.
Saurari Karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum