Tsohon gwamnan jihar Filato a jamhuriya ta biyu kuma shugaban PDP na farko Chief Solomon Daushep Lar ya rasu jiya a Amurka. Lar dan shekara 80 da haihuwa ya rasu da karfe 3 na rana agogon Amurka ko kuma karfe 8 na dare agogon Najeriya.
Yabawa: Solomon Lar Ya Rasu Yana Da Shekaru 80

5
Chief Solomon Doshep Lar gwamnan farar hula na farko a jihar Filato kuma shugaban PDP na farko a duk fadin Najeriya.