Shamsu Habibu Sani Madakin Gini wanda aka fi sai da J, jarumi ne a masana’antar Kannywood, ya ce kimanin shekaru biyar yana masana’antar, kuma ya shigeta ne domin taimakawa mutane wajen nusar da su dabi’u na malam bahaushe inda yake cewa ba shi da wata hanyar isar da sakonni face ta hanyar nishadi.
Ya ce daga cikin kalubalen da ke cewa masana’antar tuwo a kwarya shine yadda ake fifita mata wadanda suke shigowa harkar fim , sannan a mafi yawan lokuta baki ne daga wasu jihohi suke kuma aikata wasu dabi’u da ya saba da ta malama Bahaushe , kuma hakan ke kawo nakasu ga masana’antar.
Ya kara da cewa da yawan lokuta idan aka samu sabani ko wani laifi maimakon shugabannin Kannywood su tsawatar masu sabanin haka ne ke faruwa, sakamakon kasancewarsu mata sai su sakar musu ba tare da daukar hukuncin da ya da ce ba.
Ya kara da cewa yana ba da gudunmuwarsa ta hanyar fim, inda yake daukar wasu dabi’u na fadakarwa a lokaci guda kuma yake nishadantar, musammam ma yanayi na gurbacewar al’umma na shaye-shaye da sace-sace- da tabarbarewar dabi'un matasa.
Shamsu ya ce rashin ilimi na taimakawa wajen koma bayan al’umma sannan ya kara da cewa mafi yawan lokuta yakan fito a fagge na daba ne domin a duba yadda za’a magance matsalolin daba da shaye-shaye.
Shamsu ya kara kalubalantar shugabanin Kannywood da su zage dantse wajen tabbatar da an hukunta duk wata da ta yi laifi ba tare da sanya son zuciya ba.
Sannan ya dada jan hanakalin tabbatar da an tantance duk wanda zai shigo masana’antar tare da sanya idonu a duk abinda ke shige da fice a masana’antar.
Saurari cikakkiyar hirarsa da wakiliyar Dandalin VOA, Baraka Bashir: