Tun bayan da wani dan Majalisar Dokokin Kasar Burtaniya, Mista Tom Tugendhat, ya yi zargin cewa tsohon Shugaban Najeriya na mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, ya wawure kusan rabin kudin Najeriya da ke babban bankin Najeriya ya ruga London, aka shiga cece kuce, inda da dama ke ganin mai zargin bai ma san abin da ya ke cewa ba.
Daga cikin masu kiran lallai a bi ma Janar Gowon kadi akwai tsohon dan Majalisar Dattawan Nigeria kuma tsahon mai taimaka wa tsohon Shugaba Goodlock Jonathan kan harkokin majalisa, Sanata Mohammed Abba Aji, wanda ya ce yakamata gwamnatin tarayyar Najeriya da kanta ta da kuma Babban Bankin Najeriya su yi wa tsohon Shugaban kasar, Janar Yakubu Gowon adalci wajen wanke shi daga zargin na Dan Majalisar Burtaniya ya yi masa.
Sanata Abba Aji, wanda shi ne kuma Sakataren Kungiyar Gwamnonin Arewa Maso Gabashin Najeriya, ya ce lokacin da Gowon ya tafi wani taro a Kampala ne aka hambarar da gwamnatinsa. Kuma daga can Kampala din ne ma aka sanar da shi cewa an hanbarar da gwamnatinsa. Saboda haka, inji Sanata Aji, batun Gowon ya tafi da rabin kudin Najeria da ke babban bankin kasar zuwa London shirme ne.
Sanata Aji ya ce ‘yan tawagar Najeriya a Kampala ne ma su ka tara ma Gowon Fam dubu uku; shi kuma Shugaban Uganda na lokacin, Idi Amin, ya bai wa Gowon jirgi ya wuce Lome. Ya ce idan ba za a yaba ma Gowon saboda abubuwan da ya yi ma Najeriya ba, to bai kamata a bar wani ya masa irin wannan sharrin ba. Da aka ce masa baya ganin mai zargin ya yi amfani ne da ‘yancinsa na fadin albarkacin baki, sai Sanata Aji y ace mai zargin bai da makama ko hujja.
Ya ce bayan da Gowon ya dawo ma Naira dubu saba’in da biyar (N75,000) kawai aka gani a asusun ajiyarsa na banki.
Ga Haruna Dauda da cikakken rahoton: