Wani Shugaban matasan Najeriya mai suna Alhaji Gujungu ya yi kira ga Shugaban Najeriya Muhmmadu da ya sa matasa cikin gwamnatinsa ganin rawar da matasa ke takawa a harkokin gina kasa. Da ya ke hira da abokin aikinmu Usman Kabara, Alhaji Gambo Gujungu ya amsa cewa a baya an bai wa wasu matasa damar taka rawa a gwamnati amma sun gaza. To amma ya ce akwai kuma wadanda su ka yi aiki tukuru. Don haka y ace bai kamata a ki tafiya da matasa ba a wannan marran, tun da so ake a ciyar da Najeriya gaba.
Ya matasan da su ka kasa katabus yayin da aka ba su damar taka rawa, mutane ne da aka ba su matsayi haka kwatsam ba tare da sun shirya ma aikin ba. Ya ce ko su ma ba su wuce kashi 25% ba. Ya ce sama da kashi 70% su na aiki sosai. Gujungu y ace kodayake Ministan Matasa Mr. Solomon Dalung ya zarce shekarun zama matashi na daga shekaru 18 zuwa 35, ya na shiga harkokin matasa sosai. Ya ce idan aka bai ma matasa shugabancin Najeriya a 2019 za su aikata abubuwa da daman a ciyar da kasar gaba.
Ga cikakken rahoton: