Wakilin dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafar Arsenal Granit Xhaka, ya bayyana cewar dan wasan, ya amince ya koma kulob din Hertha Berlin ta kasar Jamus.
An samun takun-saka na rashin jituwa tsakanin Xhaka da kuma tsohon kocin Arsenal da ta sallama Unai Emery, tun a cikin watan Nowambar bana bayan da aka cire Granit Xhaka, a matsayin kyaftin, sakamakon wasu kalamai da ya yi, hakan ne ya sa ake alakanta shi da barin Arsenal.
Sai dai sabon kocin Arsenal Mikel Arteta, ya sanya dan wasan a cikin wasan da Arsenal ta yi da Bournemouth, inda suka tashi 1-1 a ranar Alhamis da ta gabata a gasar Premier League.
A kan wannan batu tuni wakilin dan wasan mai suna Joel Noguera, ya ce an kulla yarjejiniya kan komawar dan wasan zuwa Hertha Berlin, a watan Janairun 2020, inda yanzu kawai ake batun biyan kudi ga Arsenal.
Facebook Forum