Kungiyar Wikileaks ta saki bayanan sirrin kafofin difilomasiyyar Amurka da suka nuna cewa shugban Sudan Omar al-Bashir ya saci dala milyan dubu tara daga kudaden man kasar.
Bayanan sirrin da jaridar Guardian ta buga yace babban mai gabatar da kara a gaban kotun kasa da kasa Luis Omreno Ocampo,ya gayawa jami’an difilomasiyyar Amurka cewa al-Bashir ya boye kudaden a wani asusunsa dake bankin Lyods na Ingila.
Bayanan sun nuna Mr.Ocampo,wanda tuni yake farauntar Mr. Bashir kan laifuffukan yaki, yana cewa farin jinin Mr.Bashir zai zube da zarar jama’a sun fahimci irin yawar dukiya da ya boye.
Shi dai Mr. Bashir bai fito fili ya yi magana kan wan nan zargi ba,amma wasu manyan kusoshin gwamnatinsa biyu sun fito sun ce,kalaman Mr. Ocampo ba gaskiya bace.