A Najeriya, 'yar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Kaltungo, da Shongom a jihar Gombe, hajiya Binta Bello, ta kaddamar da wani shiri na taimakawa matan karkara guda dari shida ta hanyar koya musu sana’o’i dabam dabam da za su taimaka wajen rage masu radadin talauci.
Sana’o’in na hannu da za a koyawa matan sun hada da koyon yin man shafawa, da sabulu, da sabulun wanke gashi, da turare, da sauransu. Wannan shirin dai an kaddamar da shine da zummar taimakawa matan su sami abin dogaro da kai.
Wani magidanci shi ma ya yaba da wannan shirin. Yana mai cewa “ba mata kadai zai amfana ba, su ma zai taimaka masu gaya, don haka cigaban su ne”.
Hajiya Binta Bello, ta ce shirin zai koyawa mata sana’o’i bakwai a yankin, don tallafa. Ta kuma ce kusan miliyan ashirin za a yi amfani da su wajen tafiyar da shirin.
Facebook Forum