Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kungiyar Kare Hakkin Bil Adam Ta Ce Za Ta Sake Kalubalantar Tinubu A Kotu


Lokacin da Tinubu ya ziyarci Buhari a fadarsa a Abuja.
Lokacin da Tinubu ya ziyarci Buhari a fadarsa a Abuja.

A farkon makon da ya gabata Tinubu yai kai wa Buhari ziyara a fadarsa inda ya fada masa burinsa na tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

Wata kungiyar kare hakkin bil adama da lamuran siyasa da ake kira Concern Nigeria for the Protection of Human Rights and Rule of Law, ta ce za ta farfado da wata kara da ta shigar kotu akan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas.

Yayin wata hira da ya yi da Peter Clottey a shirin "Nightline Africa" na Muryar Amurka, jami'i a kungiyar kare hakkin bil adaman Deji Adeyanju ya ce bai dace a bar Tinubu ya tsaya takara ba.

Hakan na zuwa ne bayan Tinubu ya bayyana shirin tsayawa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa, wanda aka tsara a shekarar 2023.

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da ya yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa da ke Abuja, babban birnin kasar.

Ana dai yaba masa da taka rawar gani wajen kafa jam’iyyar APC da kuma nasarar da jam’iyyar ta samu a zabukan da suka gabata.

Sai dai kungiyar ta ce a hana tsohon gwamnan jihar Legas tsayawa takara.

Kungiyar ta ba da misali da wata hira inda Tinubu ya yi ikirarin mallakar wasu kudade da ke kunshe a cikin manyan motoci biyu a gidansa – wanda hakan ya saba wa manufofin kudin Najeriya.

Manufar ta hana mutane yin amfani da kudi fiye da Naira miliyan biyar (ko $12, 069).

Sai dai magoya bayan tsohon gwamnan sun ce ’yan kungiyar makiya ne da ke gudanar da taron jama’a don su yi suna. Sun ce Tinubu bai taka wata doka ba.

A farkon makon da ya gabata Tinubu ya fadawa manema labarai cewa ya sanar da shugaba Muhammadu Buhari aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.

“Ina da kwarin gwiwa, hange, da kwarewar iya mulki da zan dora akan turakun da shugaban kasa ya kafa don samarwa Najeriya makoma ta gari, na taba yi a jihar Legas.” Tinubu ya ce yayin taron manema labarai.

XS
SM
MD
LG