Ita Majalisar Dokokin Kanon tace ta dakatar da binciken ne saboda sanya bakin wasu manya da suka hada da tsoffin shugabannin kasar da attajirai da sarakuna.
A cikin wadanda suka sa baki akwai Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdulsalami Abubakar dukansu tsoffin shugabannin Najeriya da suke zaune a Minna fadar gwamnatin jihar Neja.
Dangane da wannan batun dakatar da binciken na Sarkin Kano da kuma shiga tsakani da manyan mutane suka yi ya sa Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu mazauna jihar Neja.
Onarebul Ahmed Dogara tsohon dan majalisar dokokin jihar yace gara da manya suka shiga tsakani saboda babu dadi a ce 'yan majalisa sun samu sarki da wani abun da bai dace ba. A ganinsa ba wai sarkin ya danne hakkin talakawa ba ne. Kudin da aka ce ya kashe ya yiwa talakawansa aiki ne.
Wata Jamila mazaunar Minna ita ko cewa tayi bata ji dadin dakatar da binciken ba. Injita da an cigaba da binciken domin ya wanke kansa. Tace yanzu ana iya cewa idan babban mutum yayi wani abu ba za'a bincikeshi ba.
Amma shugaban kungiyar IZALA reshen jihar Neja Alhaji Abdullahi Musa Mai Rediyo nasiha ce ya yiwa sarkin.Yace a matasiyinsa na malami, masanin ilimin zamani kuma attajiri ya san idan hakkin talakawa na hannunsa kuma ya danne gobe kiyoma sai ya biya. Idan ko akwai abu makamancin hakan ya mayarwa masu shi domin ya samu tsira duniya da lahira.
Kokarin jin ta bakin tsoffin shugabannin kasa dake zaune a Minna bai ci nasara ba. Shi Janar Abdulsalami Abubakar an ce yayi tafiya zuwa kasar Habasha. Amma ana cigaba da kokarin jin ta bakin Janar Ibrahim Badamasi Banagida akan lamarin na Sarkin Kano.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.
Facebook Forum