Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu ‘Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Mata Uku A Karamar Hukumar Madagali dake Jihar Adamawa


 Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo
Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Jibrilla Bindo

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne suna ci gaba da satar mata a Karamar Hukumar Madagali dake cikin jihar Adamawa, kamar yadda suka sake sace wasu mata uku jiya a kauyen Magar, lamarin da Mr. Adamu Kamale dan majalisar wakilan tarayya dake wakiltar yankin ya tabbatar

Rahotanni na cewa wadannan ‘yan bindiga masu tada kayar bayan sun yi awon gaba da ‘yan mata uku a kauyen Magar dake cikin karamar hukumar Madagali a arewacin jihar Adamawa yayin da suka je aiki a gona.

Magar dai nada tazaran tafiyar kilomita 25 ne daga Gulak shedikwatar Karamar Hukumar Madagali, wacce aka kwato daga hannun yan Boko Haram a shekarar 2015.

Koda yake kawo yanzu, duk kokarin ji daga bakin kakakin rundunan soji ta 28 dake Mubi, Manjo Badare Akintoye abun ya ci tura don ko na ta buga wayarsa ba ‘a dauka ba,to sai dai kuma dan majalisar wakilai dake wakiltar Madagali da Michika, Mr Adamu Kamale ya tabbatar da lamarin inda ya bayyana halin zulumin da suke ciki a yanzu.

Ga rahoton Ibrahim Abdul'Aziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG