Bayanai daga yankin Diffa a Jamhuriyar Nijar na cewa da faduwar rana jiya Laraba wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai hari kan barikin sojan Tumur.
An shafe lokaci mai tsawo ana bata-kashi tsakanin sojojin barikin da 'yan bindigan kafin 'yan bindigan su juya su koma inda suka fito.
Wani Manmadu Kaka Tuda, mazaunin garin, ya yiwa Muryar Amurka bayani akan lamarin. Ya ce abun asha shi ne 'yan bindigan sun kashe sojoji hudu. Sun jikata mutane tara, takwas cikinsu sojoji ne dayan kuma ma'aikacin jinya ne. Mutane taran suna asibitin Diffa.
Baicin wannan harin 'yan bindigan, inji Kaka Tuda, sun kone ma'aikatar kansiloli kuma sun kone wani wurin a barikin sojojin Diffan. 'Yan bindigan sun yi awan gaba da wasu motocin sojoji da makamai.
Kawo yanzu gwamnatin kasar Nijar ba ta ce komi ba. Shi ma gwamnan jihar Diffa Dandano Muhammad da Muryar Amurka ta tuntuba ya bukaci a yi hakuri har zuwa karfe biyar zuwa shida na yammacin yau Alhamis.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani
Facebook Forum