A cewar kungiyar ala'ummar Bauchi basu san abun dake faruwa a gwamnatac ba.
Yakubu Alhaji Jibrin skataren kungiyar yace yanzu an ciwo bashin wasu kudade kimanin nera miliyan dubu hudu da ba'a san abun da za'a yi dasu ba.Yakubu ya yi ikirarin suna da shaidar an karbo bashin daga bankn UBA.
Lokacin da gwamnan ya hau mulki yace ya gaji bashi na nera biliyan 125 amma kuma sai gashi ya je ya kara cin bashi. Yakubu ya yi zargin cewa kowane wata gwamna ya ba matansa nera miliyan uku duk da cewa ofishinsu baya cikin kundun tsarin mulkin Najeriya ko na jiha..
Amma shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dokokin jihar Yakubu Shehu Abdullahi yace gwamnan ya samu amincewar majalisar kafin ya ciwo bashin. Wai a cikin kasafin kudin da gwamnan ya gabatar masu ya nuna zai bada wata kwangila. Sai da majalisa ta amince da kasafin kudin kafin gwamnan ya bada kwangilar.
Inji Yakubu Abdullahi gwamnan ya gaji bashi kuma dole ne ya ci bashi ya biya bashi. Wajibi ne ya ciwo bashin kuma majalisa ta amince da hakan.
Ga karin bayani.