Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon yayi Allah wadai da harin da akai jiya Lahadi kan wani sansanin majalisar a arewacin Mali, har mutane uku suka mutu wasu 12 kuma suka ji rauni.
A cikin sanarwa daMr. Ban ya bayar a daren jiya Lahadi yace, kashe sojan kiyaye zaman lafiya da fararen hula a Mali, keta dokar kasa da kasa ce, da ba za'a lamunta dashi ba".
Magatakardan yace "kokari a fili na hana a sami ci gaba a dai dai wannan muhimmin lokaci da ake yunkurin samun zaman lafiya a Mali, abun bakin ciki ne", inji Mr. Ban.
Majalisar Dinkin Duniya tace an harba rokoki fiyeda da 30 a kan gidan da sojojin kiyaye zaman lafiyan suke a yankin Kidal a Mali. Haka nan makaman sun dira kan rugar larabawa makiyaya dake kusa, inda yara biyu suka halaka.
Jami'ai suka ce sojojin kiyaye zaman lafiyar, basu bata lokaci ba wajen maida martani. Babu bayanai nan take kan wadanda suke da alhakin kai wannan hari da aka yi a safiyar jiya Lahadi.