Ma'aikatan dake tare da hukumar tsaron farin kaya wato Nigeria Civil Defense Corps ko NCDC a takaice a jihar Neja sun ce sun shiga halin tangaririya.
Ma'aikatan sun shiga halin da suke ciki ne a sakamakon yadda suka ce an ki tabbatar dasu a matsayin ma'aikatan hukumar tun a shekarar 2004. Har ya zuwa wannan lokacin ma'aikatan suna anfani da rigunan kaki na hukumar da katin shaida na zama ma'aikatan hukumar.
Masana harkokin shari'a sun ce lamarin babban hadari ne ga kasa. Abdullahi Ahmed Shiroro ya yi magana a madadin tawagar. Yace suna nan su ne ma'aikatan hukumar na sa kai. Wai idan aiki ya zo su ne suke zuwa yin aikin.
Kodayaushe hukumar take son tantancesu suna zuwa cikin kayan aikinsu ne. Duk wata suna ba kowane dayansu nera dubu talatin. Kakakin nasu yace su dari hudu ne kuma sunayensu na nan a Abuja. Tabbatar dasu ma'aikatan hukumar ne ya cutura.
Mr. Philip Ayuba kwamanadan hukumar na jihar Neja yace shi bai san da zamansu ba. Yace wadanda su ne ma'aikatan sa kai na ainihi gwamnati ta riga ta basu aiki na dindindin. Yace masu aikin sa kai ba dole ba ne a biyasu ko a daukesu aiki.
Wani masanin shari'a Barrister Abdulmalik Sarkin Daji yace lamarin nada hadari. Idan har mutanen ba ma'aikata ba ne amma gasu da rigar sarki da katin shaida to yaudara ta shigo ciki duk da cewa a shari'ance mutanen basu da hujja..
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.