Duk da amincewarsu sun ce yanayin kunci da ake ciki ba zai dore ba domin za'a shawo kanshi.
Wani Malam Ahmed Yusuf tsohon babban darakta a bankin Unity yace an shiga wannan mawuyacin halin ne domin gwamnatocin baya basu yi wani tanadi ba dangane da kudaden shiga da aka dinga samu a can baya.
Dalili na biyu shi ne faduwar darajar mai da farashinsa a kasuwannin duniya. Idan farashinsa bai sake tasowa ba haka lamarin zai cigaba.
Yace a tsarin da gwamnatin Buhari ta fito dashi dole ne mutanen kasar su fara shuka abun da suke ci. Kayan masarufin da kasar ke anfani dasu su kasance abun da 'yan kasa suka shuka ne suka sarafa ba wai an shigo dasu daga waje ba.
Ta hanyar noma gwamnati ta fara aiki yadda ya kamata fata nan shi ne noman ya dore amma dole a jira lokacin da za'a fara samun albarkatun noma.
Na biyu a samo kudin shiga koda ma bashi za'a ci a baza cikin jama'a za'a samu masalaha musamman idan an yi anfani dashi ta hanyar da ta kamata domin gujewa wata matasalar kuma.
Abu na uku a jawo jihohi su tsaya tsayin daka su kula da tattalin arziki domin a samu fita da wuri.
Dr Obadiah Mailafiya tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya yace rashin samun kwararru dake ba shugaban kasa shawara akan tattalin arziki ya sa aka shiga mawuyacin hali kamar wannan. Gwamnati bata da kungiyar masana tattalin arziki da take aiki dasu.
Ga karin bayani